Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin bam na 1996 kan ginin Khobar Towers a kusa da Dhahran, Saudiyya. A ranar 25 ga watan Yunin 1996, mambobin Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah) suka tashi bam da ke jikin mota a wurin ajiye motoci na ginin Khobar Towers, wani rukunin gidaje da da sojojin Amurka ke zaune a ciki. Fashewar ta tarwatsa gini mafi kusa tare da kashe dakarun Amurka 19 da kuma wani ɗan Saudiyya, kuma ya raunata ɗaruruwan ‘yan ƙasashe da dama.
A ranar 21 ga watan Yunin 2001, wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya gano laifin mutum 14 da ke da hannu a harin. Daga cikin waɗanda aka gano akwai Ahmad Ibrahim al-Mughassil, da Abdelkarim Hussein Mohamed al-Nasser, da Ibrahim Salim Mohammed al-Yacoub, da Ali Saed bin Ali el-Hoorie, waɗanda Lada Don Adalci ke ba da tayin dala miliyan 5 don samun bayanai kan kowannensu.