Taliban a Pakistan (Tehrik-e Taliban Pakistan – TTP) ƙungiyar ta’addanci ce ta Pakistan da Afghanistan da aka kafa a 2007. TTP Muradun TTP Shine ta fitar da gwamnatin Pakistan daga Lardin Khyber Pakhtunkwa (wacce a baya take ƙarƙashin gwamnatin tarayya)da ƙirƙiro tsarin shari’a ta hanyar ta’addanci. TTP ta koyi aƙida daga al-Ka’ida (al-Qa’ida – AQ), yayin da wasu mambobin AQ ke dogara da TTP wajen samun mafaka a kan iyakar Pakistan da Afghanistan. Hakan ya baiwa kungiyar TTP damar samun dabarun kungiyar al-Qa’ida da kuma kwarewar mambobin ƙungiyar.
TTP ta kai hare-hare kuma ta ɗauki alhakin hare-haren ta’addanci kan kadarorin Amurka da na Pakistan, ciki har da na watan Disamban 2009 na ƙunar-baƙin-wake kan sansanin sojan Amurka a Khost, Afghanistan wanda ya kashe Amurkawa bakwai, da wani harin na Afrilun 2010 na ƙunar-baƙin-wake kan ƙaramin ofishin jakadancin Amurka a Peshawar, Pakistan da ya kashe ‘yan Pakistan shida. An zargi TTP da hannu kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Firaministan Pakistan Benazir Bhutto a 2007. TTP ta jagoranta da kuma yunƙurin kai harin bam da bai yi nasara ba kan dandalin Times da ke New York ranar 1 ga watan Mayu na 2010.
A ranar 1 ga Satumban 2010, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana TTP a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima, da kuma Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana TTP taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da TTP. Laifi ne mutum ya samar da gangan ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa TTP kayan aiki da gangan.