Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan Sirajuddin Haqqani, wanda aka sani da Siraj Haqqani and Khalifa. Sirajuddin ya jagoranci Haqqani Network (HQN), wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. HQN ta shirya tare da ƙaddamar da manyan hare-hare da kuma garkuwa da mutane kan dakarun Amurka da ƙawayenta a Afghanistan, da kuma kan gwamnatin Afghanistan da fararen hula. A 2015 aka naɗa Sirajuddin mataimakin shugaban Taliban, abin da ya ƙarfafa ƙawancen HQN da Taliban.
Yayin wata hira da wata kafar yaɗa labarai ta Amurka, Sirajuddin ya amsa cewa shi ne ya shirya harin ranar 14 ga Janairun 2008 kan otel ɗin Serena da ke Kabul da ya kashe mutum shida, cikinsu har da Ba’amurke Thor David Hesla. Sirajuddin ya kuma amsa shirya yunƙurin kashe Shugaban Ƙasar Afghanistan Hamid Karzai a Afrilun 2008.
A ranar 11 ga watan Maris na 2008, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Sirajuddin a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Sirajuddin taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Sirajuddin. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa HQN kayan aiki da gangan.