Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai kan jagoran ISIS-K Shahab al-Muhajir. A watan Yunin 2020, jagororin ISIS suka naɗa al-Muhajir, wanda aka sani kuma da suna Sanaullah Ghafari, don ya jagoranci ISIS-K, wadda Amurka ta naɗa a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje. Wata sanarwa da ke ɗauke da naɗin nasa ta bayyana al-Muhajir a matsayin jagora a aikin soja kuma ɗaya daga cikin “zakunan ISIS-K” a Kabul wanda aka sha damawa da shi a hare-haren sari-ka-noƙe da kuma shirya hare-haren ƙunar-baƙin-wake. Mutumin da aka haifa a shekarar 1994 a Afghanistan, shi ne ke da alhakin ba da umarnin aiwatar da ayyukan ISIS-K a faɗin Afghanistan da kuma ɗaukar nauyin Kai hare-hare.