Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah.
Nazem Said Ahmad shahararren mai halasta kuɗin haram ne da ke zaune a Lebanon kuma mai ɗaukar nauyin Hizballah.
Ahmad na cikin manya da ke taimaka wa Hizballah da kuɗi ta hanyar daɗaɗɗiyar alaƙarsa da kasuwancin haramtaccen gwal. Hizballah na amfani da Ahmad da kamfanonisa wajen halasta maƙudan kuɗin da ake bai wa ‘yan ta’adda. Ya zuwa ƙarshen 2016, ana kallon Ahmad a matsayin babban mai ɗaukar nauyin Hizballah da ke halasta kuɗin haram ta cikin kamfanoninsa da kuma samar da kuɗaɗe ga babban shugabann Hizballah, Hasan Nasrallah. Ana kuma zargin Ahmad shiga harkokin safarar haramtaccen gwal, kuma a baya ya yi kasuwanci a Belgium inda ya dinga tallafa wa Hizballah.
Ahmad kan ajiye kuɗaɗensa ta hanyar sayen kadarori a fannin zane-zane masu daraja da zimmar rage raɗaɗin takunkuman da Amurka ta saka masa, sannan ya buɗe wata cibiyar adana zane-zane a Beirut don halasta kuɗin haram. Ahmad na da hamshaƙin rumbun tara zane-zane da suka kai darajar miliyoyin dala, ciki har da ayyukan Pablo Picasso da Andy Warhol, waɗanda da yawansu aka kafe a cibiyar tasa da kuma gidansa da ke Beirut. Ahmad na ɓoye sawun haramtacciyar dukiyarsa ta hanyar tura maƙudan kuɗaɗe a lokakci guda ta bayan fage. Domin ya hana gwamnatin Lebanon ganin dukiyarsa, Ahmad ya haramta wa ƙasar da mutanenta maƙudan kuɗaɗen da ya kamata ya biya a matsayin haraji yayin da ƙasar ke fama da matsalolin tattalin arziki.
A ranar 13 ga watan Disamban 2019, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Ahmad a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, saboda taimakawa da ɗaukar nauyi ta hanyar samar da kuɗi ko kuma kayan aiki ga Hizballah. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Ahmad taɓa duk wata dukiya da ya mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Ahmad. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.