Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Muhammad al-Jawlani, wanda aka sani da Abu Muhammad al-Golani da Muhammad al-Julani. Al-Jawlani na jagorantar al-Nusrah Front (ANF), ƙawar al-Qa’ida (AQ) a Syria. A watan Janairun 2017, ANF ta haɗa kai da wasu ƙungiyoyin adawa masu tsauri, inda suka kafa ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS). Duk da cewa al-Jawlani ba shi ne shugaban HTS ba, har yanzu wani babban jagora ne a ANF, wada ke ƙawance da AQ wadda kuma ke kan gaba a HTS.
A ƙarƙashin jagorancin al-Jawlani, ANF ta kai hare-hare da dama na ta’addanci a faɗin Syria, inda take yawan harar fararen hula. A watan Afrilun 2015, an ruwaito cewa ANF ta yi garkuwa da wasu fararen hula Ƙurdawa kusan 300 a wani wurin duba ababe hawa amma ta sake su daga baya. A watan Yunin 2015, ANF ta ɗauki alhakin kashe mazauna ƙauyen Druze 20 da ke Qalb Lawzeh a Gundumar Idlib, Syria.
A watan Afrilu na 2013, al-Jawlani ya yi mubaya’a ga shugaban AQ Ayman al-Zawahiri. A Yulin 2016, al-Jawlani ya yabi AQ da al-Zawahiri cikin wani bidiyo sannan ya ce ANF za ta sauya sunanta zuwa Jabhat Fath Al Sham (“Mamayar Lardin Syria”).
A ranar 16 ga watan Mayun 2013, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Jawlani a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Jawlani taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da al-Jawlani. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa ANF kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.