Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan biyar don samun bayanai kan Muhammad Ahmed al-Munawar, wanda aka sani da Abdarahman al-Rashid Mansour da Ashraf Naeem Mansour. Ana zargi Al-Munawa da kasancewa mamban ƙungiyar ta’addanci ta Abu Nidal Organization, kuma ana nemansa ne saboda rawar da ya taka a garkuwa da jirgin Pan Am Flight 73 a Karachi, Pakistan ranar 5 ga Satumban 1986. Bayan tsare fasinjoji 379 da ma’aikatan jirgin tsawon awa 16, sai masu garkuwar suka fara harbi kan mai tsautsayi. Mutum 20 ciki har da Amurkawa biyu aka kashe sannan aka raunata fiye da 100.
Saboda rawar da ya taka a garkuwar, wani rukunin masu taimaka wa alkali a Amurka ya ce al-Munawar na da laifi kuma yana cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema. Ana tunanin al-Munawar na zaune a Gabas ta Tsakiya.