Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai da za su kai ga lalata harkokin kuɗi na Hizballah. Mohammad Ibrahim Bazzi da ke kasuwanci a sassan Belgium, da Lebanon, da Iraq, da sauran ƙasashe a Afirka ta Yamma, babban mai ɗaukar nauyin Hizballah ne. Bazzi ya tara wa Hizballah miliyoyin daloli daga harkokin kasuwancinsa.
Bazzi ya mallaka ko kuma yana tafiyar da kamfanonin Global Trading Group NV, Euro African Group LTD, Africa Middle East Investment Holding SAL, Premier Investment Group SAL Offshore, da kuma Car Escort Services S.A.L Kamfanonin da ke dandariyar ƙasa, baki ɗayansu na ƙarkashin takunkumi da Amurka ta sanya musu waɗanda da su ne Bazzi ya samar wa Hizballah miliyoyin dala.
A ranar 17 ga watan Mayun 2018, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Mohammad Ibrahim Bazzi a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Bazzi taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da Bazzi. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.