Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Mohamed Makawi Ibrahim Mohamed. Shi ne jagoran harin da ya kashe ma’aikatan agaji na hukumar Agency for International Development (USAID), John Granville da Abdelrahman Abbas Rahama a Khartoum ranar 1 ga Janairun 2008. Makawi na da alaƙa da wata ƙungiya a Sudan da ake kira Al-Qa’ida a Ƙasashen Kogin Nilu Biyu (Al-Qa’ida in the Land of the Two Niles) wadda ta ƙudiri aniyar kai wa kadarorin Amurka da na Sudan da na ƙasashen Yamma hari.
Wata kotun Sudan ta yi wa Makawi shari’a, ta kama shi da laifi, har ma ta yanke masa hukuncin kisa a 2009 saboda hannunsa a kisan. Sai dai kuma, Makawi ya gudu daga gidan yari ranar 10 ga watan Yunin 2010 kafin a zartar masa da hukuncin. Har yanzu ba a kama shi ba kuma ana kyautata zaton yana kasar Somaliya.
A ranar 8 ga watan Janairun 2013, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Makawi a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Makawi taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Makawi.