Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Maalim Salman, wani babban jagoran al-Shabaab, wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya. Tsohon shugaban al-Shabaab marigayi Ahmed Abdi Godane ya zaɓi Salman ya jagoranci mayaƙan ƙungiyar ‘yan ƙasar waje a Afirka. Wanda aka sani kuma da Maalim Salman Ali da Ameer Salman, Salman ya sha shiga hare-hare a Afirka da ake kai wa masu yawon buɗe-ido, da wuraren nishaɗantarwa, da kuma coci-coci. Duk da cewa ya fi mayar da hankali kan ayyuka a wajen Somalia, an san Salman yana zaune a Somalia, inda yake ba wa mayaƙa ‘yan ƙasar waje horo saboda tura su sauran wurare. A ranar 24 ga Satumban 2014, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Salman a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Salman taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Salman. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa al-Shabaab kayan aiki da gangan.
Maalim Salman
Afirka – Kudu da Hamadar Sahara