Lashkar-e Tayyiba (LeT), wadda aka sani kuma da Army of Righteous, ƙungiyar ‘yan ta’adda ce a Pakistan da aka kafa a shekarun 1980. LeT ta aikata abubuwa, ciki har da manyan hare-hare kan sojojin Indiya da kuma fararen hula tun 1993. Kazalika, ƙungiyar ta kai wa sojojin ƙawance hari a Afghanistan. LeT ce ke da alhakin kai harin ta’addanci na 2008 a Mumbai na Indiya da ya kashe mutum 166 –ciki har da ‘yan Amurka shida –kuma ya raunata mutum fiye da 300.
A ranar 26 ga watan Disamban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana LeT a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 20 ga watan Disamba na 2001 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana LeT matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana LeT taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da LeT. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa LeT kayan aiki.