Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Khalil al-Rahman Haqqani, wanda aka sani da Khalil Haqqani ko Khalil Ahmad Haqqani. Khalil ya yi aikin a matsayin babban jagoran Haqqani Network (HQN), wadda Amurka ta ayyana matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje.
Khalil ya shiga ayyukan tattara wa Taliban kuɗi sannan ya ba wa Taliban taimako wajen gudanar da ayyuka a Afghanistan. Daga farkon 2010, ya samar wa gidajen yari na Taliban kuɗi a Gundumar Logar da ke Afghanistan. A 2009, Khalil ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda ska dinga kama mutane ƙarƙashin Taliban da kuma HQN. Khalil ya gudanar da ayyuka a madadin Taliban bisa umarnin ɗan uwansa Sirajuddin Haqqani, babban jagoran HQN kuma mataimakin shugaban Taliban. Khalil ya kuma yi wa al-Qa’ida (AQ) aiki sannan an alaƙanta shi da ayyukan ƙungiyar. A 2002, ya tura ƙarin dakaru don ƙarfafa AQ a Gundumar Paktia, Afghanistan.
A ranar 9 ga watan Fabarairun 2011, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Khalil a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Khalil Haqqani taɓa duk wata dukiya ko kadarorida ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Khalil Haqqani. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa HQN kayan aiki da gangan.