Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan on Jehad Serwan Mostafa, wanda aka sani da Ahmed Gurey, Anwar al-Amriki, da Emir Anwa. Mostafa na da shaidar zama ɗan Amurka kuma mazaunin California a baya, wanda ya riƙe muƙaman shugabanci a al-Shabaab, wadda Amurka ta ayyana matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje. An yi imanin shi ne ɗan Amurka mafi girman muƙami da ke aiki da ƙungiyar ta’addanci a ƙasashen waje.
Mostafa ya zauna kuma ya kammala karatun kwaleji a San Diego, California kafin ya koma Somalia a 2005. An yi imanin cewa ya ba da gudummawa a hari kan sojjin Ethiopia kafin ya shiga al-Shabaab a wuraren shekarar 2008. Tare da al-Shabaab, Mostafa ya yi aiki a matsayi daban-daban masu muhimmanci, ciki har da mai horar da ayyukan soja a sansanin ƙungiyar, ya jagoranci mayaƙa ‘yan ƙasar waje a sashen yaɗa labarai, ya shiga tsakanin al-Shabaab da wasu ƙungiyoyin ta’addanci, sannan ya yi jagoranci a wasu hare-haren ƙungiyar da bam. An yi imanin cea har yanzu Mostafa na ci gaba da shirya hare-hare a kan gwamnatin Somalia da kua dakarun da ƙungiyar haɗin kan Afirka ke mara wa baya a Somalia da Gabashin Afirka. Sakamakon haka, Mostafa na ci gaba da yi wa dakarun Amurka barazana da fararen hula da ma kadarori.
A ranar 9 ga watan Oktoban 2009, an gano laifin Mostafa a California kan tuhumar da ake yi masa na haɗin baki wajen samar wa ‘yan ta’adda kayan aiki, da kuma haɗa baki waje samar wa al-Shabaab kayan aiki, da ma taimaka wa al-shabaab. A ranar 2 ga Disamban 2019, an gabatar da tuhuma mafi girma kan Mostafa a kotun tarayya ta Amurka, inda aka tuhume shi da zargin ta’addanci. Mostafa na cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema.