Jamaat-ul-Ahrar (JuA) ƙungiyar gwagwarmaya ce da ke da alaƙa da (Taliban a Pakistan (Tehrik-e Taliban Pakistan – TTP), wadda Amurka ta ce ta ta’addanci ce a ƙasar waje. Ƙungiyar da tsohon shugaban TTP Abdul Wali ya kafa a 2014, JuA ta kai hare-hare da dama a Pakistan kan fararen hula, da mabiya addinai marasa rinjaye, da dakarun soja, da jami’an tsaro. A watan Agustan 2015, JuA ta ɗauki alhakin kai harin ƙunar-baƙin wake a Punjab, Pakistan da ya kashe Ministan Harkokin Cikin Gida Shuja Khanzada da kuma magoya bayansa 18. JuA ce ke da alhakin kashe ‘yan Pakistan biyu ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Peshawar a farkon Maris na 2016. A ƙarshen watan Maris na 2016, JuA ta kai harin ƙunar-baƙin-wake kan wurin shaƙatawa na Gulshan-e-Iqbal a Lahore da ke Pakistan, wanda ya kashe mutum 70 – kusan rabinsu mata ne da yara – kuma ya jikkata wasu ɗaruruwa.
A ranar 3 ga watan Agustan 2016, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana JuA a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana JuA taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da JuA.