Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Ibrahim Taher mai ɗaukar nauyin Hizballah ne da ke ayyukansa a ƙasar Guinea. An bayyana Taher a matsayin ɗaya daga cikin mafiya shahara na masu ɗaukar nauyin Hizballah a Guinea. An yi imanin cewa ya ɗauki mutane da dama aiki da ke bin Hizballah a cikin ƙasar.
Taher da wani abokin kasuwancinsa sun aika da dalar Amurka da suka karɓa daga ɗaya daga cikin wuraren kasuwancinsu zuwa filin jirgi na Conakry inda suka bai wa jami’an kwastam na Guinea cin hanci don su ƙyale a wuce da tsabar kuɗin nasu. Taher ya yi amfani da matsayinsa na jami’in difilomasiyyar Lebanon a ƙasar Cote d’Ivoire wajen kauce wa bincike a lokutan da yake shiga da fita daga Guinea.
A 2020, wani rukunin ‘yan Lebanon da kasuwanci a Guinea, cikinsu har da Taher da kuma wani mai tallafa wa Hizballah Ali Saade, suka isa Lebanon a jirgi ɗauke da manyan kuɗaɗe. ‘Yan kasuwar sun yi iƙirarin cewa kuɗin na tallafin annobar korona ne a Lebanon don su kauce wa sa ido. An sha yin amfani da tallafin korona a matsayin wata hanya wajen aika wa Hizballah kuɗi daga Guinea zuwa Lebanon.
A ranar 4 ga watan Maris na 2022, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Taher a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima, saboda taimakawa da ɗaukar nauyi ta hanyar kuɗi ko kuma samar da kayan aiki ga Hizballah. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Taher taɓa duk wata dukiya da ya mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Taher. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje.