Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Ibrahim Salih Mohammed al-Yacoub. Al-Yacoub wanda ake zargi da kasancewa mamban Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah), ana neman sa ne saboda hannunsa a harin bam na 1996 kan ginin Khobar Towers da ke kusa da Dhahran na Saudiyya.
A ranar 25 ga watan Yunin 1996, mambobin Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah) suka tada bam da ke jikin mota a wurin ajiye motoci na ginin Khobar Towers, wani rukunin gidaje da da sojojin Amurka ke zaune a ciki. Fashewar ta tarwatsa gini mafi kusa tare da kashe dakarun Amurka 19 da wani ɗan Saudiyya, kuma ya raunata ɗaruruwan ‘yan ƙasashe da dama.
A ranar 21 ga Yunin 2001, wani rukunin masu taimaka wa alƙali ya ce al-Yacoub da wasu 13 na da alaƙa da harin.
A ranar 12 ga watan Oktoban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Yacoub a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Yacoub taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da al-Yacoub. Yana cikin jerin sunayen ‘ya ta’addan da FBI ta fi nema.