Hurras al-Din (HAD) ƙawar alƘa’ida ce da ɓulla a Syria a farkon 2018 bayan ɓangarori da dama sun ɓalle daga Hayat Tahrir al-Sham (HTS).
A ranar 10 ga Satumban 2019, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana HAD a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana HAD taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da HAD.