Hizballah ƙungiyar ta’addanci ce a Lebanon da ke samun makamai da horo, da kuma tallafi daga Iran, wadda Sakataren Harkokin Waje ya siffanta da cewa ƙasar da ke ɗaukar nauyin ta’addanci a 1984. Hizballah na da girma sosai kuma iat ce ke da alhakin kai manyan hare-hare da dama. Sun haɗa da: harin 1983 na ƙunar-baƙin-wake kan ofishin jakadancin Amurka a Beirut; hari kan barikin sojan Amurka na Marine Corps Barracks; harin 1984 kan ofishin jakadancin Amurka a Beirut; da kuma yin garkuwa da jirgin TWA Flight 847 a 1985. An gano Hizballah tare da Iran na da hannu a harin 1992 kan ofishin jakadancin Isra’ila a Argentina da kuma na 1994 kan ƙungiyar taimakon Yahudawa ta Jewish Mutual Aid Society da ke Buenos Aires. A 2012, Hizballah ta yi nasarar kai harin ƙunar-baƙin-wake a Bulgaria. Jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin Hizballah da kuma shirye-shirye a ƙasashe kamar; Azerbaijan, Cyprus, Egypt, Kuwait, Nigeria, Peru, da Thailand.
A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Hizballah a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Daga baya kuma, a ranar 31 ga Oktoban 2001 Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Hizballah matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana Hizballah taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da Hizballah. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa Hizballah kayan aiki.