Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Hassan Afgooye, jagoran ƙungiyar ta’addanci ta al-Shabaab. Afgooye na jagorantar wani tsarin harkokin kuɗi da ya ƙunshi haɗa gidauniyar boge da ajo da garkuwa da mutane don tallafa wa al-Shabaab, wadda Amurka ta ayyana matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. An kallon Afgooye a matsayin mai muhimmanci a harkokin ƙungiyar.
Hassan Afgooye
Afirka – Kudu da Hamadar Sahara