Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Hasib Muhammad Hadwan, wanda kuma aka sani da Hajj Zayn, babban jami’i ne a Babbar Sakatariyar Hizballah. Mataimaki ne ga Hasan Nasrallah, babban sakataren na Hizballah, kuma aikinsa shi ne tattaro kuɗi daga hannun masu ba da tallafi da ‘yan kasuwa da ke wajen Lebanon. Daga cikin ayyukansu, Hadwan da manajan ofishinsa Ali al-Sha’ir, na amfani da tsarin tura kuɗi na duniya wajen aika kuɗi zuwa Lebanon ta hanyar ɓoye manufarsu wadda ita ce ɗaukar nauyin ƙungiyar ta’addanci.
A ranar 17 ga Satumban 2021, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Hadwan a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Hadwan taɓa duk wata dukiya da ya mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da Hadwan. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.