Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance

Harin Bam Kan Ofisoshin Jakadancin Amurka (Kenya da Tanania)

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Lada

Up to $5 million

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin bam na 1998 kan Ofishin Jakadancin Amurka a Kenya da Tanzania. A ranar 7 ga watan Agustan 1998, mambobin ƙungiyar al-Qa’ida (AQ) suka tashi bam a ofisoshin jakadancin Amurka na Nairobi da Dar es Salam lokaci guda. Hare-haren sun kashe mutum 224 kuma suka jikkata wasu fiye da 5,000, sannan suka yi mummunar ɓarna ga ginin ofishin da maƙwabtansa.

A Nairobi, ‘yan ta’adda sun tada bam a wata mota maƙare da bama-bamai a kusa da wurin ajiye ababen hawa na ofishin, wanda ya kashe mutum 213 – ciki akwai ma’aikatan ofishin 44 (12 Amurkawa, 32 kuma ‘yan sauran ƙasashe) – da kuma raunata wasu fiye da 5,000, ciki har da Jakadan Amurka Prudence Bushnell.

A Dar es Salam, ‘yan ta’adda da ke tuƙa mota cike da bama-bamai sun yi yunƙurin kutsa wa ƙofar ofishin, suka harbi masu gadi sannan suka tayar da bama-baman. Fashewar ta kashe mutum 11 tare da jikkata wasu 85.

An yi wa waɗannan mutanen da ke jere nan ƙasa shari’a tare da yanke musu hukunci a kotun tarayya ta Amurka:

  • Mamdouh Mahmud Salim, a founding member of AQ, was arrested in September 1998 in Germany and extradited to the United States. He is serving a life sentence in prison for his connection to the bombings.
  • In October 2001, AQ operatives Wadih El-Hage, Khalfan Khamis Mohamed, Mohamed Rashed Daoud Al-Owhali, and Mohamed Sadeek Odeh were convicted on charges of planning and executing the bombings and sentenced to life in prison.
  • In January 2011, AQ operative Ahmed Khalfan Ghailani was convicted and sentenced to life for his role in the bombings.
  • In September 2014, Adel Abdel Bari, a close associate of AQ leader Ayman al-Zawahiri, pleaded guilty to conspiring to kill U.S. nationals and received a 25-year prison sentence. He was released from prison in 2020.
  • In May 2015, Khaled al-Fawwaz, deputy to now-deceased former AQ leader Usama bin Ladin, was sentenced to life in prison for his connection to the attacks.

Wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya gano hannun Abdullah Ahmed Abdullah, da Anas al-Libi, da Mohammed Atef, da Usama bin Ladin a hare-haren. Dukkan tsoffin shugabannin AQ sun mutu yanzu.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada don neman bayanai kan jagoran AQ Sayf al-Adl, wanda aka gano laifinsa kan rawar da ya taka a hare-haren bam kan ofisoshin jakadanci.

Hotuna:

Fasta-Fasta:

Wuraren da Ke Da Alaƙa:

Kenya, Tanzania

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Please open your Line app to submit a tip. The number is +1 202 702 7843

Please open your Viber app to submit a tip. The number is +1 202 702 7843

Please visit our Tor-based tips-reporting channel at: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Signal don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Line don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Telegram don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Viber don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Ku duba shafin da zai ba ku ƙarin bayani game da turo rahoto a: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Skip to content