Shirin Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don neman bayanai kan Mohamoud Abdi Aden, da duk wani da ke da hannu a harin dqa al-Shabaab ta kai a 2019 kan otle ɗin DusitD2 a Nairobin Kenya. Da tsakar 15 ga watan Janairun 2019, mayaƙan al-Shabaab ɗauke da manyan makamai da gurneti da sauran abubuwan fashewa suka kai hari a cibiyar kasuwanci ta DusitD2, wanda ya ƙunshi rrukunin gidaje shida mai ɗauke da shaguna da ofisoshi da kuma otel. Aƙalla mutum 21 ne, ciki har da Ba’murke, aka kashe a harin. Al-Shabaab – mai alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta al-Ƙa’ida – ta dinga nuna harin kai-tsaye a shafinta na Shahada News Agency kuma ta ba da sanarwa cewa shugaban al-Ƙa’ida na lokacin Ayman Zawahiri ne ya ba da umarnin kai harin.
Wani jagoran al-Shabaab mai suna Aden ne ya shirya harin na Janairun 2019. A ranar 17 ga watan Oktoban 2022, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana shi a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya a ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima.
Al-Shabaab ce ke da alhakin kai hare-haren ta’addanci da dama a Kenya, da Somaliya, da kuma maƙwabtansu tare da kashe dubban mutane, ciki har da Amurkawa. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya a watan Maris na 2008. A watan Afrilun 2010, Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC) ya sake ayyana al-Shabaab a ƙarƙashin yarjejeniya ta 1844 (2008).