Haqqani Network (HQN) ƙungiyar ‘yan gwagwarmaya ce da ke aiki a Afghanistan da Pakistan bayan kafa ta a ƙarshen shekarun 1980. HQN ta shirya tare da ƙaddamar da manyan hare-hare da kuma garkuwa da mutane kan dakarun Amurka da ƙawayenta a Afghanistan, da kuma kan gwamnatin Afghanistan da fararen hula. A watan yunin 2012, wani harin ƙunar-baƙin wake da HQN ta kai kan sansanin sjan Amurka a Khost da ke Afghanistan ya kashe sojan Amurka biyu da kuma raunata wasu fiye da 100. Jami’an gwamnatin Afghanistan sun zargi HQN da kai harin ƙunar-bakin-wake a watan Mayun 2017 da mota a Kabul wanda ya kashe mutum fiye da 150. An yi imanin cewa HQN ce ta kai harin watan Janairun 2018 da wata motar ɗaukar marasa lafiya a Kabul da ya kashe mutum sama da 100. Kazalika, gwamnatin Afghanistan ta zargi HQN da laifin kai harin 2018 kan otel na Intercontinental a Kabul da ya kashe mutum 22.
A ranar 19 ga watan Satumban 2012, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana HQN a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 7 ga watan Satumban 2012 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana HQN matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana HQN taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da HQN. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa HQN kayan aiki da gangan.