Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta al-Shabaab. Harkokin kuɗi na al-Shabaab na taimaka mata wajen ci gaba da ayyuka da kuma ɗaukar nauyin hare-haren da ka jawo mutuwar dubban fararen hula da kuma jami’an tsaro a Somaliya da ƙasashe maƙwabta.
Al-Shabaab na bin hanyoyin da aka saba da su na ta’addanci wajen ɗaukar nauyin harkokinta, kamar ba da cin hanci, da ƙwace, da tura kuɗi ta dandalin hawala, da yin garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa, da halasta kuɗin haram, da kuma ɗaiɗaikun mutane, sai dai ita ma ta ƙirƙiri hanyoyin samun kuɗinta na musamman kuma tana ƙara dogara da kanta. Ɗaya daga cikin sabbin hanyoyin samun kuɗinta shi ne ƙwace a hannun manyan mutane, da ‘yan kasuwa, da manoma: amfani da kasuwar ababen hawan da aka yi amfani da su, tura kuɗi ta wayar salula, da kuma satar kayan makiyaya. Ta hanyar kama sabbin garuruwa, al-Shabaab kan shiga haramtattun harkoki kamar haƙar ma’adanai ta ɓarauniyar hanya da kuma safarar kayayyaki kamar gawayin coal, da tabar wiwi (da take sayar wa ƙungiyoyin miyagu), da hauren giwa, da amfanin gona, da kuma sikari. Kazalika, al-Shabaab kan saka wa mutane haraji, da harkokin kasuwanci, da matuƙa jirgin ruwa da sauransu, sannan su karɓi kuɗaɗe daga afanin gona da na gonaki.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na ba da tayin lada don samun bayanai da za su kai ga ganowa da kuma kawo ƙarshen harkokin:
–babbar hanyar samun kuɗin al-Shabaab (misali, ƙwace da karɓar haraji, safarar haramtattun kayayyaki da makamai, da kasuwancin ƙwayoyi)
–amfani da ma’adanan ƙarƙashin ƙasa da al-Shabaab ke yi (kamar sare bishiyoyi, da haƙar ma’adanai, da sumoga)
–gudunmuwa a ɗaiɗaikun mutane ke bayarwa da kuma shige wa al-Shabaab gaba
–babbar hanyar harkokin kuɗi da cibiyoyin kuɗi ke yi da kuma yin amfani da fasahohin aika kuɗi don turawa ko kuma samun shiga harkokin kuɗi na duniya da wasu ke yi a madadi al-Shabaab
–kasuwanci ko hannayen jari da al-Shabaab ta mallaka ko take juyawa ko kuma masu ɗaukar nauyinta
–ayyukan kamfanonin ƙasa da ƙasa da ke da alaƙa da al-Shabaab, da ke gudanar hada-hadar kuɗi a madadinta (kamar kasuwancin tsofaffin ababen hawa)
–haramtattun harkoki da suka ƙunshi mambobin al-Shabaab da magoya bayanta, waɗanda ke amfanar da ƙungiyar (kamar yin garkuwa don karɓar kuɗin fansa da kuma ƙwacen kayayyakin makiyaya)
–haramtattun harkokin kuɗi na al-Shabaab (kamar halasta kuɗin haram), da tura kuɗaɗe ko kaya da al-Shabaab ke yi zuwa ga ƙawayenta ‘yan ta’adda da abokan hulɗa
Ranar 18 ga watan Maris na 2008, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a natsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Daga baya, a ranar 19 ga watan Maris na 2008 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a natsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224 da aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana al-Shabaab taɓa duka dukiya ko kadarori da ta mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, kuma an haramta wa dukkan Amurkawa yin hulɗar kuɗi da al-Shabaab. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa al-Shabaab kayan aiki.