Sakamakon Adalci na tayin ladan dala miliyan 10 domin bada bayanai akan Hafiz Saeed, shi ya kafa kuma shine shugaban Lashkar-e Tayyiba (LeT), wadda Amurka ta ayyana a matsayin Kungiyar ‘yan ta’adda ta kasar waje (FTO). Saeed yana cikin waɗanda suka shirya kai hari har na kwana 4 wanda ya faru a Mumbai, Indiya a watanNuwamba 2008 wanda ya kashe mutane guda 166, harda ‘yan Amurka guda shida.
A shekarar 2020, kotu mai hana ta’addanci ta hukunta Saeed akan wasu munanan abubuwa masu yawa akan ta’addanci aka kuma tura shi kurkuku. Ƙasar Amurka ta ci gaba da neman bayanai akan Saeed soboda tsarin shari’a na Pakistan sun saki mutanen LeT da shugabansu da suka kama a baya.
A 27 ga watan Mayu , 2008, Ma’aikatar Ajiyar kuɗaɗe ta ƙasar Amurka ta ayyana Saeed a matsayin mai Ta’addanci da aka zayyana musamman a duniya bisa umarnin zartarwa na 13224, kamar yadda aka gyara. Sakamakon wannan ayyanawar da ma wasu abubuwa da suka biyo baya, an rufe duk wasu dukiyoyi da kadarori da makamantan abubuwa mallakar Saeed waɗanda ke cikin hurumin ƙasar Amurka, kuma an hana ‘yan ƙasar Amurka baki-ɗaya yin kowace irin hulɗa da Saeed. Bugu da ƙari, ya zama babban laifi mutum ya samar ko kuma yayi yunƙurin da wasu makamai cikin sani ko ma a haɗa kai da shi wajen samar da makamai ko kayan aiki ga ƙungiyar FTO LeT. A 10 ga watan Disamba , 2008, Majalisar ɗinkin duniya sun sa sunan Saeed a 1267/1989 in ji hukumar na saka takunkumin al-Qa’ida a mutum mai haɗa kai da ƙungiyar ta’addanci, kuma a maimakon haka, yana buƙatar takunkumin a duniya baki daya.