Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 2 don samun bayanai kan Hafiz Abdul Rahman Makki, wanda aka sani da Abdulrahman Maki. Maki ya riƙe muƙamai daban-daban a Lashkar-e-Tayyiba (LeT), wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO). Ya kuma taka rawa wajen samar wa LeT kuɗaɗen gudanar da ayyuka.
A 2020, wata kotun hukunta laifukan ta’addanci ta hukunta Makki kan uhuma ɗaya ta laifin ɗaukar nauyin ta’addanci kuma ta tura shi gidan yari. Amurka na ci gaba da neman bayanai kan Makki saboda tsarin shari’ar Pakistan ya saki wasu mambobin LeT waɗanda aka ɗaure a baya.
A ranar 4 ga watan Nuwamban 2010, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Makki a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Makki taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Makki. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa LeT.kayan aiki da gangan.