Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai da za su kai ga lalata harkokin kuɗi na ƙungiyar ta’addanci ta Daular Islama a Iraƙi da Syria (ISIS). ISIS ta dogara ne kan gungun ‘yan kasuwa da masu tallafa mata wajen gudanar da ayyukanta da kuma kai hare-hare a Syria da kewayen yankin.
Gungun ‘yan ISIS sun tura kuɗaɗe don tallafa wa ƙungiyar kan ayyukanta a sansanonin ‘yan gudun hijira na cikin gida bayan sun karɓi kuɗin a Indonesia da Turkiyya, waɗanda aka yi amfani da wasu daga ciki wajen safarar yara daga sansanonin da zimmar miƙa su ga mayaƙan ISIS na ƙasashen waje don mayar da su mayaƙa.
Masu goyon bayan ISIS a ƙasashe fiye da 40 sun tura wa ƙungiyoyi masu alaƙa da ISIS ɗin kuɗi a irin waɗannan sansanoni don tallafa wa farfaɗowarta. A sansanin al-Hawl – mai ƙunshe da mutum 70,000 wanda kuma shi ne mafi grima a arewa maso gabshin Syria – mayaƙn ISIS sun samu dala 20,000 duk wata ta hanyar hawala, wata haramtacciyar hanyar tura kuɗi, kuma akasarin kuɗin sun fito ne daga wajen Syria ko kuma sun biyo ta ƙasashe maƙwabta kamar Turkiyya.
Haramtattun harkoki ta hanyar safarar kayan tarihi daga Syria da Iraq, su ne manyan hanyoyin samun kuɗi da ke ba wa ISIS damar kai hare-hare da zalintar fararen hula. Satar kayayyakin tarihi da lalata su da ISIS ke yi a Syria da Iraq sun sa an rasa kayayyakin tarihi na rayuwar mutanen baya.
Tsoffin silalla na tarihi, da sarƙoƙi, da duwatsu, da mutum-mutumi, da gumaka, da allunan rubutu na cikin abubuwan tarihi da ISIS ta yi safararsu. Cibiyar adana kayan tarihi ta ƙasa da ƙasa ta International Council of Museums tare da taimakon Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ta samar da wani tsarin gaggawa na gano kayayyakin da aka sace daga Syria da Iraq.