Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan gungun masu garkuwa da mutane na ISIS ko kuma bayanan da za su kai ga ganowa da ƙwatowa da dawo da Maher Mahfouz, Michael Kayyal, Gregorios Ibrahim, Bolous Yazigi, da kuma Paolo Dall’Oglio.
A ranar 9 ga watan Fabarairun 2013, wani mai wa’azin Kirista na Girka Maher Mahfouz da mai wa;azin ɗariƙar Katolika ɗan Armenia Michael Kayyal na kan hanyarsu ta zuwa wani gidan tarihi a Kafrun da ke Syria cikin motar bas ta haya. Nisan kusan kilomita 30 daga birnin Aleppo na Syria, wasu da ake zargin ‘yan ISIS ne suka tsayar da motar, suka duba takardun shaida na fasinjoji, sai kuma suka fito da Mahfouz da Kayyal daga bas ɗin. Tun daga wannan lokacin ba a sake jin ɗuriyarsu ba.
A ranar 22 ga Afrilun 2013, mai wa’azin gargajiar Kiristanci Archbishop Gregorios Ibrahim ya yi balaguro daga Aleppo zuwa Turkiyya don ya ɗauko mai wa’azin gargajiyar Kiristanci Archbishop Bolous Yazigi. Lokacin da suka isa wani wurin duba ababen hawa a kusa a al-Mansoura, Syria, wasu mutane ɗauke da makamai suka tare su kuma suka ƙwace motar. Daga baya an ga gawar direban motar. An yi imanin cewa wasu mayaƙa ne masu alaƙa da al-Nousra Front, wadda ƙawar al-Ka’ida ce, uka sace su. Sai dai kuma daga baya an miƙa wa ISIS malaman.
A ranar 29 ga watan Yuli na 2013, ISIS ta yi garkuwa da mai wa’azi ɗan Italiya mai suna Paolo Dall’Oglio a Raqqah na Syria. Dall’Oglio ya shirya tattaunawa da ISIS don a sako Mahfouz da Kayyal da Ibrahim da Yazigi. Ba a sake jin ɗuriyarsa ba tun daga lokacin.