Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Fuad Mohamed Khalaf, wanda aka sani kuma da Fuad Shongale. Khalaf jagora ne na al-Shabaab kuma ya sama wa ƙungiyar kuɗaɗe, wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO).
A watan Afrilun 2008, Khalaf da wasu mutane da dama suka jagoranci wani harin mota cike da baam-bamai kan sansanonin Ethiopia da na Gwamnatin Riƙon Ƙwarya ta Somalia a Mogadishu, Somalia. A watan Mayu na 2008, Khalaf da wani gungun mayaƙa suka kai hari tare da kama wani ofishi ‘yan sanda a Mogadishu, inda suka kashe da kuma raunta sojoji da dama. A watan dai, Khalaf ya shirya ajo har sau biyu don tallafa wa al-Shabaab a masallatan Kismayo na Somalia.
A ranar 13 ga watan Afrilun 2010, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta sanya Khalaf a matsayin Ayyanannen Ɗan Ƙasa bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13536 saboda ba da gudummawa wajen ta da hankali da lalata harkokin tsaro a Somalia. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Khalaf taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Khalaf. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa al-Shabaab kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.