Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Faruq al-Suri, wanda kuma aka sani da Samir Hijazi ko Abu Hammam al-Shami. Al-Suri ne shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Hurras al-Din (HAD) kuma ƙwararren mamba a al-Ka’ida (AQ).
Al-Suri tsohon jami’in tsaro ne mai ba da horo tare da jagoran AQ a Afghanistan, Sayf al-Adl a shekarun 1990, kuma ya horar da mayaƙan AQ a Iraq daga 2003 zuwa 2005. An taɓa tsare Al-Suri a Lebanon daga 2009 zuwa 2013 kuma daga baya ya zama kwamandan soja a ƙungiyar al-Nusrah Front (ANF). Ya ba ANF a 2016.
A ranar 10 ga Satumban 2019, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Suri a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Suri taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da al-Suri.