Daular Islama ta Iraqi da Syria (Islamic State in Iraq and Syria – ISIS) ta ɓulla ne daga ɓurɓushin al-Qa’ida a Iraqi (al-Qa’ida in Iraq – AQI). Ƙungiyar ta laƙaba wa kanta sunan ISIS ne saboda bayyana muradanta yayin da take faɗaɗa ayyuka don shigar da rikicin Syria. Abu Bakr al-Baghdadi ne shugaban ISIS, wanda ya ayyana kafa daular Musulunci a watan Yuni na 2014. An kashe shi ranar 27 ga watan Oktoban 2019 lokacin da sojojin Amurka suka yi yunƙurin kama shi. ISIS ta yi amfani da rikicin Syria da kuma tashin hankali a Iraqi, abin da ya sa ta samu damar ƙwace iko da wasu yankuna a ƙasashen biyu. A 2019, wani ƙawancen ƙasashen duniya don yaƙar ISIS – da yahaɗa ƙasashe da yawa da kuma cibiyoyi – ya ƙwace dukkan wuraren da ISIS ke iko da su a Syria da Iraqi. An ci gaba da yaƙar ƙungiyar a Syria da Iraqi da sauran ƙasashe.
A Nuwamban 2015, ISIS ta kai wasu jerin hare-hare a Paris da ya kashe mutum kusan 130, ciki akwai ɗan Amurka, sannan ya jikkata fiye da mutum 350. A watan Maris na 2016, ISIS ta jagoranci hare-hare biyu a Brussels da suka yi sanadiyyar kashe mutum 32 ciki har da ‘yan Amurka huɗu, sannan suka jikkata fiye da 250. A Yunin 2016, wani ɗn bindiga da ya yi mubaya’a ga ISIS ya kashe mutum 49 tare da raunata wasu 53 a wani gidan casu na mai suna Pulse a Orlando da ke jihar Florida. A Yulin 2016, ISIS ta ɗauki alhakin kai hari wanda wani ɗan ta’adda da ke tuƙa motar ɗaukar kaya ya kai wa taron mutane hari a Nice na Faransa yayin bikin Bastille Day, abin da ya haddasa kisan mutum 86, ciki har da ‘yan Amurka uku. A Janairun 2019, ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ƙunar-baƙin-wake kan wani wurin cin abinci a Manbij na Syria da ya kashe mutum 19, ciki har da Amurkawa huɗu. A ranar Lahadin Ista ta 2019 a Sri Lanka, an kashe mutum fiye da 250, ciki har da Amurkawa biyar, lokacin da masu biyayya ga ISIS suka ƙaddamar da shiryayyun hare-hare a coci-coci da otel-otel.
A ranar 17 ga watan Disamban 2004, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQI (ISIS a yanzu) a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 15 ga watan Oktoba na 2004 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQI matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana ISIS taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da ISIS. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa ISIS kayan aiki da gangan.