An kafa Daular Islama ta Iraqi da Syria a Yankin Sahara ko ISIS A Babban Yankin Sahara (ISIS in the Greater Sahara – ISIS-GS) a 2015 bayan ta ɓalle daga al-Mourabitoun, wadda ta ɓalle daga al-Qa’ida, kuma ta yi mubaya’a ga ISIS. Ƙungiyar da asalinta shi ne Mali da kuma gudanar da ayyukanta a kan iyakar Mali da Nijar, tana kuma yin ayyuka a Burkina Faso. (ISIS-GS) ta ɗauki alhakin kai hare-hare da dama, ciki akwai na ranar 4 ga Oktoban 2017 kan wani sintiri na haɗin gwiwa tsakanin Nijar da Amurka a yankin Tongo Tongo da ke Nijar, wanda ya jawo kisan sojan Amurka huɗu da na Nijar huɗu. A Nuwamban 2019, ISIS-GS ta kai hari kan sansanin sojan Mali da ya kashe sojoji 54.
A ranar 23 ga Mayun 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-GS a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 16 ga watan Mayun 2018 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-GS matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana ISIS-GS taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da ISIS-GS. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa ISIS-GS kayan aiki da gangan.