Dakarun Tsaro na Neman Sauya Hali na Musulunci – Rundunar Qods (Islamic Revolutionary Guard Corps-Qods Force – IRGC-QF), wani ɓangare na IRGC, wata hanya ce da Iran ke amfani da ita wajen haddasawa da kuma taimaka wa ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasashen waje. Iran na amfani da IRGC-QF wajen cimma muradinta na ƙasashen waje, tana shinge ta wajen ayyukan leƙn asiri, sannan ta ƙirƙiri rikici a yankin Gabas ta Tsakiya. A 2011, IRGC-QF ta shirya kashe jakadan Saudiyya a Amurka a birnin Washington D.C. A 2012, an kama mambobin IRGC-QF a Turkiyya da Kenya saboda shirya hare-hare. A Janairun 2018, Jamus ta gano wasu ma’aikatan IRGC 10 da ke hannu wajen shirya kai hare-hare a ƙasar.
Ranar 15 ga Afrilun 2019, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana IRGC da IRGC-QF a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. A 2017, Sashen Bailtul-Malin Amurka ya ayyana IRGC matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima, saboda taimaka wa IRGC-QF. Sakamakon haka, an hana IRGC taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da IRGC. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa IRGC kayan aiki da gangan.