Dakarun Neman Sauya Hali na Musulunci (Islamic Revolutionary Guard Corps –IRGC), wani ɓangare na rundunar sojan gwamnatin Iran ne da ke taka rawa wajen amfani da ta’addanci a matsayin babbar hanyar cimma muradun ƙasar. IRGC na tsarawa da jagoranta da kuma aiwatar da ta’addanci a faɗin duniya. Haka nan, IRGC ta ƙirƙiri wasu ƙungiyoyin ta’addanci da ba su taimako da kuma horarwa. IRGC ce ke da alhakin kai hare-hare daban-daban kan Amurkawa da gine-ginen Amurka, ciki har da waɗanda suka kashe ‘yan Amurkar. Tun bayan kafa ta a 1979, IRGC ta taka rawa wajen aiwatar da manufar Iran a ƙasashen waje. Rundunar na iko da ɓangare mai girma na tattalin arzikin Iran kuma tana da tasiri kan siyasar cikin gida a Iran.
A ranar 15 ga watan Afrilun 2019, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana IRGC da IRGC-Qods Force a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. A 2017, Sashen Bailtul-Malin Amurka ya ayyana IRGC matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima, saboda taimaka wa IRGC-QF. Sakamakon haka, an hana IRGC taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da IRGC. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa IRGC kayan aiki da gangan.