Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Aziz Haqqani, wanda kuma aka sani da Abdul Aziz Haqqani. Aziz babban jagora ne na Haqqani Network (HQN ), wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO), kuma ɗan uwa ga shugaban HQN da mataimakin shugaban Taliban Sirajuddin Haqqani.
Akwai hannun Aziz a shiryawa da aiwatar da hare-haren bam kan kadarorin gwamnatin Afghanistan, kuma shi ne ya rungumi kai manyan hare-haren HQN bayan mutuwar ɗan uwansa Baruddin Haqqani. Aziz na cikin dukkan ayyukan haɗa bama-bamai da kuma ba da umarni a hare-haren HQN kan dakarun Afghanistan da sojojin ƙawance a kan iyakar Afghanistan da Pakistan. Bugu da ƙari, ya yi aiki a matsayin zuciyar HQN wajen gudanar da ayyuka a birnin Kabul da kuma manyan hare-hare a faɗin Afghanistan.
A ranar 25 ga watan Agustan 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Aziz Haqqani a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Aziz Haqqani taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Aziz Haqqani. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa HQN kayan aiki da gangan.