Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai kan mutanen da ke da alhakin kai harin ranar 26 ga watan Agustan 2021 na ta’addanci a babban filin jirgi na birnin Kabul da ke Afghanistan. Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kai harin ne lokacin da Amurka da sauran ƙasashe ke shirin kwashe ‘yan ƙasarsu masu yawa da kuma wasu ‘yan Afghanistan masu rauni. Mutum aƙalla 185 aka kashe a harin, cikinsu har da dakarun Amurka 13 da ke taimaka wa aikin kwashewar. An kuma jikkata mutum fiye da 150 da suka haɗa da dakarun Amurka 18. ISIS-K wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje, ita ce ta ɗauki alhakin kai harin.