Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Ali Youssef Charara, wanda aka sani da Ali Youssef Sharara da ‘Ali Yusuf Sharara, babban mamba ne a ƙungiyar Hizballah kuma mai ɗaukar nauyinta, shi ne kuma shugaban kamfanin sadarwa na Spectrum Investment Group Holding SAL da ke Lebanon, wanda Ma’aikatar baitul-Malin Amurka ta saka wa takunkumi. Charara ya karɓi miliyoyin dalar Amurka daga Hizballah don ya juya su a wasu harkokin kasuwanci da za su amfani ƙungiyar ta’addancin.
Ƙari a kan ƙoƙarinsa na samar wa Hizballah kuɗi, Charara ya yi kasuwancin man fetur a Iraq. Bugu da ƙari, Charara na da kadarori a harkokin sadarwa a Yammacin Afirka.
A ranar 7 ga watan Janairun 2016, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Charara a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Charara taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Charara. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.