Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan biyar don bayanai kan Ali Sayyid Muhamed Mustafa al-Bakri, wanda kuma aka sani da Abd al-Aziz al-Masri. Al-Bakri mamba ne majalisar shura ta al-Qai’da (AQ), wadda ke yanke hukunci, kuma babban abokin jagoran AQ Sayf al-Adl. Al-Bakri ƙwararre ne wajen haɗa bama-bamai.
Kafin ya shiga AQ, al-Bakri mamba ne a Ƙungiyar Jihadin Musulunci ta Masar (Egyptian Islamic Jihad) ta ta’addanci ƙarƙashin jagorancin al-Zawahiri. Ya yi aiki a matsayin mai koyarwa a sansanin AQ na Afghanistan, inda ya horar da sabbin ‘yan ta’adda wajen amfani da bama-bamai da makamai masu guba. Al-Bakri ya kuma yi yunƙurin yin garkuwa da wani jirgin saman fasinja na Pakistan a Disamban 2000. Akwai yiwuwar yana ci gaba da horar da ‘yan ta’adda na AQ da sauran masu tsattsauran ra’ayi.
Al-Bakri na zaune da iyalinsa a Iran.
A ranar 3 ga watan Oktoba na 2005, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana al-Bakri a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Bakri taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da al-Bakri. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa AQ kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.