Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Ali Saade mai ɗaukar nauyin Hizballah ne da ke ayyukansa a ƙasar Guinea. Saade na aika wa Hizballah kuɗi daga Guinea ta hanyar amfani da wakilan Hizballah a Guinea da Lebanon.
A 2020, wani rukunin ‘yan Lebanon da kasuwanci a Guinea, cikinsu har da Saade da kuma wani mai tallafa wa Hizballah Ibrahim Taher, suka isa Lebanon a jirgi ɗauke da manyan kuɗaɗe. ‘Yan kasuwar sun yi iƙirarin cewa kuɗin na tallafin annobar korona ne a Lebanon don su kauce wa sa ido. An sha yin amfani da tallafin korona a matsayin wata hanya wajen aika wa Hizballah kuɗi daga Guinea zuwa Lebanon.
Ana zargin Saade da amfani da jiragen kafin kifi don gudanar da miyagun harkoki, kamar safarar ƙwayoyi.
A ranar 4 ga watan Maris na 2022, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Saade a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima, saboda taimakawa da ɗaukar nauyi ta hanyar kuɗi ko kuma samar da kayan aiki ga Hizballah. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Saade taɓa duk wata dukiya da ya mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Saade. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje.