Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Ali Qasir wakilin Hizballah ne a Iran kuma mai faɗi a ji ne a harkokin kasuwanci da ke samar wa Dakarun Tsaro na Neman Sauya Hali na Musulunci – Rundunar Qods (Islamic Revolutionary Guard Corps-Qods Force – IRGC-QF) kuɗaɗe da kuma Hizballah. Kazalika, jami’in Hizballah Muhammad Qasir kawunsa ne wanda suke aiki kafaɗa da kafaɗa wajen gudanar da harkokin kuɗi tsakanin IRGC-QF da Hizballah.
Har wa yau, Ali Qasir ne manajan kamfanin Talaqi Group da ke da alaƙa da Hizballah wanda kuma ke ɗaukar nauyinyi wa jigila IRGC-QF jigilar man fetur. Ali Qasir kan shirya jiragen da ke kai wa ƙungiyar ta’addancin mai bisa taimakon IRGC-QF. Aikin Ali Qasir ya ƙunshi tattauna farashin kayayyaki da kuma yin cinikin abubuwan da suka shafi dakon mai. Ali Qasir ya jagoranci ciniki sannan ya taimaka wajen biyan kuɗin dakon mai na Iran daga ADRIAN DARYA 1 don amfanin IRGC-QF. Ali Qasir na wakiltar kamfanin mai na Hokoul S.A.L. Offshore wajen cinikin sayar da fetur ɗin Iran ga Syria. Bugu da ƙari, Ali Qasir ya tsara tare da yin aiki tare da wasu wajen amfani da kamfanin Talaqi Group don sayar da ƙarafa na miliyoyin daloli.
A ranar 4 ga Satumban 2019, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Ali Qasir a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, baya ga sauran abubuwa, an hana Ali Qasir taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Ali Qasir. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.