Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula –AQAP) ƙungiya mai tsattsauran ra’ayi a Yemen da ta bayyana a Janairun 2009 bayan ‘yan ta’addan Saudiyya da na Yemen sun haɗe. Babban ƙudirin AQAP shi ne kafa daular Musulunci da kuma aiki da shari’a a ƙasashen Larabawa da yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya. AQAP ta kai wa kadarorin Amurka da na ƙasashen Yamma hari a ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashe. Ƙungiyar ta ɗauki nauyin kai hare-hare da dama, ciki har da na watan Janairun 2015 da ta kai kan ofishin jaridar barkwanci ta Charlie Hebdo a Paris wanda ya kashe mutum 12.
AQAP ƙawar AQ ce kuma shugaban AQAP na aiki tare da shugabannin AQ wajen tsara hare-hare. Maharin bam na AQAP al-Asiri ne ya shirya hari kan jirgin sama a Ranar Kirsimeti sannan kuma ya aika da bama-bamai a cikin injin gurza rubutu zuwa Amurka.
A ranar 19 ga watan Janairu na 2010, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQAP a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje a ƙarƙshin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa da aka yi wa kwaskwarima, da kuma ayyana ta Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224 da aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana AQAP taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadara da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da AQAP. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko taimakawa wajen samar wa AQAP kayan aiki.