Ƙungiyar da aka sani da sunan Salafist Group for Preaching and Combat al-Qa’ida (GSPC) ) in the Islamic Maghreb (AQIM) ta samu gindin zama ne bayan ta yi mubaya’a ga al-Qa’ida a 2006. Duk da cewa AQIM ta ci gaba da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel kawai, tana da aƙidar ƙin jinin Turawan Yamma.
AQIM ta sha aikata laifukan ta’addanci da dama, da suka haɗa hare-haren bam, da kai wa fararen hula hari, da kuma garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa. Harin bam da AQIM ta kai a 2007 kan hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma wani ginin gwamnatin Aljeriya ya kashe mutum 60. A Janairun 2016, AQIM ta kai hari kan wani otel a Burkina Faso da ya kashe mutum 28 tare da jikkata 56. A watan Maris na 2016, AQIM ta ɗauki alhakin kai hari a wani bakin ruwa na a ƙasar in Côte d’Ivoire da ya kashe mutum fiye da 16 sannan ya raunata wasu 33. A Janairu n 2017, AQIM ta kai harin ƙunar-baƙinm wake da ya halaka mutum sama da 50 a Gao da ke Mali.
Ranar 27 ga watan Maris na 2002, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQIM a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. A baya, a ranar 23 ga watan Satumban 2001, an saka AQIM cikin jerin Annex to Executive Order 13224, kuma daga baya tana iya fuskantar hukunci ƙarƙashin dokar saboda a matsayinta na Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya. Sakamakon haka, an hana AQIM taɓa duka dukiya ko kadarar da ta mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, kuma an haramta wa dukkan Amurkawa yin hulɗar kuɗi da AQIM. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa AQIM kayan aiki.