Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance

Ahlam Ahmad al-Tamimi

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Ahlam Ahmad al-Tamimi, wadda kuma aka sani da “Kalti” da “Halati”, a matsayin wani ɓangare na ladan da zai bayar kan shirin Tashin Hankali Don Daƙile Tattaunawar Zaman Lafiya a Gabas ta Tsakiya (hyperlink).

A ranar 9 ga Agustan 2001, al-Tamimi ta kai bam da kuma wani ɗan ƙunar-bakin-wake na Hamas zuwa wani dandazon mutane da ke birnin Ƙudus, inda maharin ya ta da bam ɗin. Harin ya kashe mutum 15, ciki har da yara bakwai. Amurkawa Judith Shoshana Greenbaum, da wata malamar makaranta mai shekara 31, da wani ɗan shekara 15 mai suna Malka Chana Roth, na cikin waɗanda aka kashe. An jikkata fiye da 120, ciki akwai Amurkawa huɗu. Hamas ta dauki alhakin kai harin.

Tsohuwar ɗalibar da ta yi aiki a matsayin ‘yar jarida, al-Tamimi ta tuƙa maharin zuwa wurin bayan ta yi alwashin kai hare-hare a madadin sashen soja na ƙungiyar Hamas wato Izzedine al-Qassam Brigades, a cewar FBI. Al-Tamimi wadda ta shirya kuma ta aiwatar da harin Sharro, ta zaɓi wurin ne saboda yana da yawan hada-hada. Don ta ɓatar da sawu, ita da maharin sun yi shiga irin ta Yahudawa kuma ita ce ta kai bam ɗin ƙunshe a cikin jakar garayar gita, daga wani gari a yamma da Kogin Jordan (West Bank) zuwa Ƙudus. Al-Tamimi ta kuma amsa cewa ita ce ta dasa wani ƙaramin bam a shagon cefane na birnin Ƙudus a matsayin gwaji kafin wannan harin.

A 2003, Al-Tamimi ta amsa laifin saka hannu a harin a wata kotun Isra’ila kuma aka yanke mata hukuncin shekara 16 a gidan yari saboda taimaka wa maharin. An sake ta a Oktoban 2011 a matsayin musayar fursuna tsakanin Isra’ila da Hamas. A ranar 14 ga watan Maris na 2017, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta janye ƙorafin tuhuma a kan Al-Tamimi da kuma umarnin kama ta. FBI ta saka ta cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda da ta fi nema.

Hotuna:

Fasta-Fasta:

Wuraren da Ke Da Alaƙa:

Jordan

Ranar Haihuwa:

20 ga Oktoba, 1980; 20 ga Nuwamba, 1980; 1 ga Janairu, 1980; 20 ga Janairu, 1980

Wurin da Aka Haife Ku:

Al-Zarqa, Jordan

Shaidar Zama Ɗn Ƙasa:

Jordan

Jinsi:

Mace

Nau’in Gashi:

Ruwan ƙasa

Nau’in Ido:

Ruwan ƙasa

Harsunan da Kuke Ji:

Larabci; Ingilishi

Sana’a:

Ɗan Jarida

Laƙabi/Yadda Kuke Rubuta Sunanku:

Ahlam Aref Ahmad Al-Tamimi; Ahlam Arafat Mazin Al Tamimi; Ahlam Arif Ahmad Al Tamimi; Ahlam Aref Ahmad Altamimi; Ahlam Arif Ahmad Altamimi; Ahlam Araf Ahmad Tamimi; Ahlam Aref Ahmad Tamimi; Ahlam Aref Ahmed Tamimi; Ihlam Araf Ahmad Tamimi; Achlam Tamimmi; Ahlam Araf Ahmed Tmimi; “Halati”; “Khalti”

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.
Skip to content