Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 7 don bayanai kan Abu Ubaydah da Yusuf al-Anabi, wanda aka sani kuma da Yazid Mubarak. Al-Anabi ne shugaban ƙungiyar ta’addanci ta al-Qa’ida a Yankin Musulman Maghreb (al-Qa’ida in the Islamic Maghreb – AQIM). AQIM ta sanar da al-Anabi a matsayin shugaban ƙungiyar a Nuwamban 2020. Al-Anabi ya yi mubaya’a ga shugaban al-Qa’ida (AQ) Ayman al-Zawahiri a madadin AQIM tare da tsammanin zai taka rawa wajen gudanar da harkokin AQ a faɗin duniya.
Al-Anabi ɗan ƙasar Algeria, tsohon shugaban Majalisar Dattiaji ne ta ƙungiyar AQIM, sannan ya yi aiki a Majalisar Shura ta AQIM ɗin. Al-Anabi ya yi aiki a matsayin shugaban sashen yaɗa labarai na AQIM.
A ranar 9 ga Satumban 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Al-Anabi a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, baya ga sauran abubuwa, an hana Al-Anabi taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Al-Anabi. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa AQIM kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. An saka al-Anabi cikin wani Ƙudirin Zauren Tsaro na Mjalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 1267 (UNSCR 1267) da ya sanya masa takunkumi ranar 29 ga watan Fabarairun 2016, wanda ya ba da damar hana shi taɓa kadarorinsa, da haramta masa balaguro, da hana shi sayen makamai.