Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan Ahmed Diriye, wanda kuma aka sani da Ahmed Umar da Abu Ubaidah. Abu Ubaidah ya yi aiki a matsayin shugaban al-Shabaab – muƙamin da ya riƙe tun bayan mutuwar tsohon shugaban al-Shabaab Ahmed Abdi Godane. Abu Ubaidah na cikin manyan ‘yan fadar Godane lokacin da shugaban ya mutu.
Kafin a maye gurbin Godane, Abu Ubaidah ya yi aiki a muƙamai da dama a al-Shabaab, ciki har da mataimakin Godane, da mataimakin gwamnan yankin Lower Juba na Somalia a 2008, da kuma gwamnan al-Shabaab a yankunan Bay da Bakool na Somalia a 2009. Zuwa 2013, shi ne babban mai ba wa Godane shawara, kuma ya yi aiki da “sashen harkokin cikin gida na al-Shabab,” inda ya sa ido kan ayyukan ciin gida na ƙungiyar. Yana da muradi irin na Godane na kai hare-haren al-Shabab a Somalia a matsayin haɓaka muradan al-Qa’ida a duniya.
A ranar 21 ga watan Agustan 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Abu Ubaidah a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Abu Ubaidah taɓa duk wata dukiya ko kadarorida ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Abu Ubaidah. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa al-Shabaab, wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje, kayan aiki da gangan.