Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanan da za su kai ga ganowa ko sanin inda Abu Ali al-Tunisi yake. Al-Tunisi babban jagora ne a ƙungiyar the Islamic State of Iraq and ash-Sham (ISIS), ƙungiyar ta’addancin da ke ci gaba da yi wa Amurka barazana da kuma kadarorinta a ƙasashen waje.
Abu Ali al-Tunisi ne jagoran ƙere-ƙere na ISIS a Iraƙi. Ya horar da mambobin ISIS kan yadda za su haɗa bama-bamai, da rigar ƙunar-baƙin-wake, da ababen fashewa. A-Tunisi ya kuma ba da babban horo kan yadda ake haɗa makamai da kuma haɗa makamai masu guba.
Abu Ali al-Tunisi na da raunuka a hannunsa na dama da idonsa na dama.
A ranar 17 ga watan Disamban 2004, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQI (ISIS a yanzu) a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima.