Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Abu ‘Abd al-Karim al-Masri, wanda kuma aka sani da Karim. Al-Masri babban mamba ne ne al-Qa’ida (Al-Qa’ida –AQ) kuma babban jagora na Hurras al-Din (HAD), ƙungiyar jihadi mai alaƙa da AQ. A 2018, al-Masri mamba ne a majalisar shura ta ƙungiyar HAD, majalisar da ke yanke hukunci kan ayyukan ƙungiyar, kuma ya yi aiki a matsayin mai shiga tsakanin HAD da ƙungiyar Hay’at Tahrir al-Sham, ƙawar AQ wadda kuma HAD ta ɓalle daga cikinta.
Abu ‘Abd al-Karim al-Masri
Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya