Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 3 don bayanai kan Abdikadir Mohamed Abdikadir, wanda kuma ake kira Ikrima. Abdikadir babban jagora ne a ƙungiyar al-Shabaab kuma ya taɓa zama shugaban sashen ayyuka na ƙungiyar. Abdikadir ya kuma taɓa tsara wasu hare-hare a baya da al-Shabaab ta kai. Ya jagoranci ɗaukar matasa a Kenya shiga al-Shabaab sannan ya zama kwamanda na rundunar mayaƙa ‘yan Kenya a Somalia.
A ranar 6 ga watan Agustan 2021, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Abdikadir a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa ga Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon wannan ayyanawa, baya ga sauran abubuwa, an hana Abdikadir taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da Abdikadir. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa al-Shabaab kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.