Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Abdelbasit Alhaj Alhassan Haj Hamad. Ana neman Abdelbasit ne saboda yana đaya daga cikin ‘yan bindigar da suka kashe JohnGranville da Abdelrahman Abbas Rahama,wađanda ma’aikata ne na hukumar ba da agaji ga kasashe ta Amurka ko U.S. Agency forInternational Development (USAID), a birnin Khartoum ranar 1 ga watan Janairu na 2008.
Wata kotu a Sudan ta yi wa Abdelbasit shari’a kuma ta kama shi da laifi, har ma ta yanke masa hukuncin kisa a 2009 saboda rawar da ya taka akisan nasu. Sai dai kuma, Abdelbasit ya tsere daga gidan yari ranar 10 ga watan Yunin 2010 kafin a zartar masa da hukuncin. Har yanzu ba a kama shi ba kuma ana kyautata zaton yana kasar Somaliya.
A ranar 8 ga Janairun 2013, an ayyana Abdelbasit matsayin Ɗan ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Kasa mai lamba13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Abdelbasit taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Abdelbasit.