Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 20 d bayanai da za su kai ga gano inda Robert A. “Bob” Levinson yake da kuma mayar da shi gida. Levinson wanda tsohon jami’in FBI ne, ya ɓata lokacin da ya yi balaguron aiki zuwa Tsibirin Kish da ke Iran ranar 9 ga watan Maris na 2007. Levinson ya yi ritaya daga FBI a 1998 kuma yana aiki da wani mai bincike mai zaman kansa a lokacin da ya ɓata.
A watan Disamban 2020, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta saka wa manyan jami’an Iran takunkumi, Mohammad Baseri da Ahmad Khazai, saboda hannunsu a sace Levinson. Amurka na ci gaba da neman bayanai kan sauran waɗanda ke da hannu cikin satar.